Rundunar ‘Yan sandan Jahar Kano ta Dakile Yunkurin Sace Mutane, ta Kama Wanda Ake Zargi

 

Hukumar ‘yan sandan jahar Kano ta yi nasarar dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane a kauyen Danzabuwa, da ke karamar hukumar Bichi.

Hakan ya kasance ne bayan ta samu korafi daga wani mutum cewa an yi masara barazana na biya wasu kudade ko kuma a sace shi ko wani daga cikin iyalinsa.

Bayan bincike an gano wani daga cikin danginsa ne ke masa barazanar inda aka kamo shi.

Rundunar ‘Yan sanda a jahar Kano ta dakile yunkurin sace mutane a kauyen Danzabuwa, da ke karamar hukumar Bichi.

Jaridar Daily Post ta rawaito cewa kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce wannan ya biyo bayan korafin da wani mazaunin Kauyen Danzabuwa, Karamar Hukumar Bichi, Jahar Kano ya shigar, cewa an tuntube shi ta waya kuma an yi masa barazanar biyan Naira miliyan daya ko kuma a sace shi ko daya daga cikin ‘ya’yansa.

Kiyawa ya ce bayan korafin, ‘yan sanda sun shiga aiki kuma sun yi nasarar cafke Tukur Ahmad mai shekaru 28, a Kauyen Panda, Karamar Hukumar Keffi, Jahar Nassarawa a ranar Asabar.

Ya ce wanda ake zargi wanda dangin mai karar ne ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu don hukunta shi.

Rundunar, duk da haka, ta ba da tabbacin ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayin zaman lafiya a jahar.

Rahoton ya kara da cewa rundunar ta kuma bukaci jama’a da su baiwa ‘yan sanda duk wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen kiyaye tsaron jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here