‘Yan Sanda Sun Harbe Fitaccen Makashi

 

‘Yan sanda sun harbi wani mutum da rundunar ke nema ruwa a jallo a Jahar Ogun.

Mutumin da ake zargin dan kungiyar asiri kuma makashi ne ya gamu da ajali bayan da yan sanda suka harbe shi.

Ya rasu yayin da yake karbar magani a gadon asibiti, sai dai hukumar ta ce ya amsa laifukan sa kafin ya mutu.

An ruwaito cewa yan sanda sun harbe wani dan kungiyar asiri kuma makashi, Owolabi Oludipe da aka fi sani da Somori a Jahar Ogun, The Punch ta ruwaito.

An harbe wanda ake zargin a musayar wuta da yan sanda ranar Lahadi, 31 ga Janairu a yankin Odogbolu da ke jihar kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda, DSP Abimbola Oyeyemi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida ranar Litinin a Abeokuta, ya ce wanda ake zargin sunan sa ya dade cikin jerin wanda hukumar ke nema ruwa a jallo tsawon lokaci.

Sunan wanda ake zargin ya shiga jerin ne biyo bayan zargin za da kashe wani jami’in Civil Defence, Rusewe Segun a Nuwambar da ta gabata. An kuma ruwaito cewa ya kashe wani Sunday Kayode Adegbuiyi a Fabarairu, 2020.

Wanda ake zargin har ila yau, shi ya kashe shugaban kungiyar asiri ta Eiye, Shoyombo Sanyaolu Fakayo a Nuwamba, 2020 lokacin rikicin wacce kungiya ce babba tsakanin biyun.

A cewar Oyeyemi, an hangi wanda ake zargin a Ita-Ado da ke Odogbolu inda shi da sauran yan kungiyar asiri ta Aiye su ke shirya sake kai hari kan mutanen yankin.

Yan sanda, da suke kokarin damke tawagar, da suka ga yan sandan, sai suka fara harbin su, yayin mayar da martani aka harbi shugaban su “Somori” kuma yaji rauni, yayin da wasu suka gudu cikin daji dauke da makaman su.

“An garzaya da shi asibiti cikin gaggawa, sai dai ya mutu lokacin da ya ke karbar magani.

“Ya amsa duk kashe kashen a gadon asibiti kafin ya mutu.

An samu wasu tarin layoyin asiri da ya sanya a gaba daya jikin sa, harsashi guda biyu da kuma wayar hannu,” a cewar Oyeyemi.

Mai magana da yawun yan sandan ya tuna da wani mashahurin makashi da ya addabi Ijebu-Ode da kewaye da jami’an tsaro suka kashe a irin wannan yanayi farkon watan da ya gabata.

Oyeyemi ta ce Kwamishinan yan sanda, Edward A. Ajogun ya umarci a sanya ido tsawon awa 24 don gano ayyukan bata gari a yankin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here