Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta Kama Bama-Bamai a Cikin Mota Kirar Mercedes Benz

Dorayi, Kano – Rundunar ‘yan sanda a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu bama-bamai a cikin wata mota kirar Mercedes Benz da ke kan hanyar Chiranchi a unguwar Dorayi a jihar Kano, rahoton Vanguard.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin makamai da alburusai da aka kwato tare da gabatar da ‘yan ta’adda tare da aka kama da laifuka daban-daban a jihar.

CP Dikko ya ce mutanensa da ke aikin bincike ne suka tare motar domin bincike, yayin da suka kan aikin binciken, wadanda ke cikin motar suka bude wuta kana suka tsere.

A cewarsa:

“Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef a yayin da jami’an leken asiri da ke sintiri a unguwar Chiranchi Dorayi Kano, a yayin gudanar da bincike sun kama wata mota kirar Mercedes Benz.

“Yayin da suke shirin tsayarwa da binciken motar, sai mutanen da ke cikinta suka bude wa ‘yan sandan wuta, inda jami’an ‘yan sandan suka yi artabu da ‘yan bindigar da suka gudu suka bar motar.”

Rahoton da muka samo ya ce, an turo jami’an kunce ababen fashewa, inda suka gano abubuwa masu hadari.

A cewarsa, an gano wadannan abubuwan; bindigogin A47 guda uku dauke da mujallu cike da alburusai casa’in, harsashi goma sha hudu na AK47, hannu daban-daban guda uku da kuma abubuwan fashewa daban-daban (IEDs).

CP Dikko ya ce:

“Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi tare kokarin kama ‘yan ta’addan.”

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here