‘Yan Sanda Sun Kama Dattijuwa Mai Shekaru 54 da Harsasai 350

 

Yobe-Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wata Hamsatu Modu mai shekaru 54 dauke da harsasan bindiga 350.

An rahoto cewa ‘yan sanda sun cafke dattijuwar ne a kauyen Morami da ke karamar hukumar Jakana Konduga ta jihar Borno.

An cafke dattijuwa da harsasai

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, inji rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta ce ana zargin Hamsatu Modu ta dauko alburusan ne daga garin Buniyadi domin kaiwa ‘yan bindiga a Yobe.

DSP Dungus ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda na ‘A’ reshen ofishin rundunar da ke Damaturu, babban birnin jihar ne suka kama wadda ake zargin.

Channels TV ta rahoto jami’in hulda da jama’ar ya ce:

“A wani bincike da aka yi cikin wata motar kirar Golf 3, jami’an sun gano harsasai masu tsayin 7.62 × 39 MM guda 350 da aka boye a cikin kayan wadda ake zargin.”

‘Yan sanda na bincikar dattijuwar

A cewarsa, rundunar ‘yan sandan ta samu sahihan bayanan sirri cewa wata da ake zargin tana safarar makamai ga ‘yan bindiga ta na kan hanyar zuwa Damaturu.

Wannan ne dalilin tsaurara matakai tare da kafa shingayen bincike, lamarin da ya kai ga nasarar cafke wadda ake zargin dauke da harsasan.

“A halin yanzu wadda ake zargin ta na fuskantar tambayoyi yayin da masu bincike ke aiki domin bankado wadanda ke daukar nauyinta da kuma makasudin safarar harsasan.”

– A cewar DSP Dungus.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here