Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Zamfara Sun Kashe Hatsabibin ‘Dan Bindiga Sun Ceto Mutane 11
Yan sanda a jahar Zamfara sun tafka gumurzu da yan bindiga a hanyar Gusau zuwa Sokoto.
Yan bindigan sun tare hanyar ne suna yi wa matafiya fashi tare da sace wasu daga cikinsu don karbar kudin fansa.
Yan sandan sun isa wurin da yan bindiga suke, suka halaka guda suka ceto mutum 11 bayan musayar wuta.
Rundunar yan sandan jahar Zamfara ta ce ta kashe wani hatsabibin dan bindiga a jahar sannan ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Kakakin yan sandan jahar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis a Gusau.
Shehu ya ce:
Read Also:
“Jiya misalin karfe 1 na rana, yan bindiga da dama sun tare hanyar Gusau zuwa Sokoto a kusa da Dogon Karfe hakan yasa matafiya suka rika neman tsira.
“Cikin kankanin lokaci jami’a yan sanda da ke sintiri a hanyar suka nufi wurin.
“Da isarsu wurin, yan bindigan suka fara harbi bayan sun riga sun kama mutane suna shirin shiga da su daji.
“Jami’an yan sandan sunyi nasara kan yan bindigan, hakan ya hana miyagun cigaba da zaluntar matafiya.”
Ya bayyana cewa yayin artabun an kashe dan bindiga daya kuma nan take aka ceto mutum 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace.
Kakakin yan sandan ya kara da cewa: “Rundunar na tsananta bincike domin ceto sauran wadanda aka sace din da yan bindigan suka shigar da su daji kafin su iso.
“An sada dukkan mutanen da aka ceto da iyalansu.”
Har wa yau, ya ce kwamishinan yan sandan jahar, Hussaini Rabiu, ya jadadda aniyarsa na ganin an kawo karshen kallubalen tsaro a jahar.