Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta Musanta Jita-Jitar Kashe Jami’inta

 

Hukumar ‘yan sanda a jihar Kano ta musanta zargin cewa an kashe daya daga cikin jami’anta.

Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu a yau Juma’a.

Ya ce jami’in dan sandan ya samu rauni ne a kai kuma yanzu an sallamo shi daga asibitin Murtala.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta rade-radin cewa an kashe dan sanda a ranar Talata 4 ga watan Yuli yayin gumurzu da ‘yan ta’adda.

Hukumar ta ce dan sandan ya samu raunuka ne yayin gumurzun a kasuwar Rimi a ranar Talata 4 ga watan Yuli.

Kakikin hukumar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu ta muryar sakon karta kwana, cewar Daily Trust.

Rundunar ta bayyana yadda abin ya faru, inda ta karyata jita-jitar

Ya ce jami’ansu sun isa wurin da ake rikicin ne don kwantar da tarzoma inda daya daga cikinsu ya samu raunuka.

Wani shaidan gani da ido a ranar ya tabbatar da kashe dan sandan, cewar rahotanni. Amma rundunar ta musanta hakan inda ta ce:

“A ranar 4 ga watan Yuli, da misalin karfe 11 na rana muka samu rahoton cewa wasu ‘yan ta’adda na fada a kasuwar Rimi inda suke kokarin kai hari kan mutane.

“Bayan samun rahoton, jami’a mu sun tura ‘yan sanda inda aka kama wasu da ake zargi guda bakwai yayin da jami’in mu daya ya samu rauni a kai.

“An kwashe shi zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda aka ba shi kulawa kuma aka sallame shi.”

Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin ci gaba da binciken sirri

Ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci kwasan wadanda ake zargin zuwa ofishin binciken laifuffuka don gudanar da binciken sirri.

Ya ce bayan kammala binciken za a tura wadanda ake zargin zuwa kotu don hukunta su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here