‘Yan Sanda Sun yi Musayar Wuta da ‘Yan Bindiga a Jahar Zamfara

 

Rundunar ‘yan sanda ta musamman da sauran jami’an tsaro sun mayar da harin da ‘yan ta’adda suka kai garin Shinkafi a jahar Zamfara.

Jami’in hulda da jama’an jahar na ‘yan sanda, SP Muhammad Shehu ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a a Gusau.

A cewarsa, sun yi musayar wuta na tsawon sa’a daya, har suka samu nasarar raunata 1 daga cikin ‘yan ta’addan yayin da sauran suka tsere da raunuka.

Shinkafi, Zamfara – Rundunar hukumar ‘yan sanda na musamman tare da hadakar sauran jami’an ta mayar da farmakin da daruruwan ‘yan bindiga suka kai garin Shinkafi, hedkwatan karamar hukumar Shinkafi ta jahar Zamfara.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, an samu wannan bayanin ne a wata takarda ta ranar Juma’a wacce jami’in hulda da jama’a, SP Muhammad Shehu ya saki a Gusau.

Shehu ya ce ‘yan bindiga wadanda ‘yan sansanin shu’umin dan bindigan nan, Turji, sun yi musayar wuta da jami’an tsaron a Shinkafi don kariya ga lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

“Bayan kammala musayar wutar wacce aka yi sa’a daya ana yi, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya samu munanan raunuka saboda alburusai, sannan sauran kuwa ta yuwu sun samu raunukan,” a cewar PPRO din.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar, Ayuba Elkanah, ya tura wasu jami’an tsaron zuwa yankin don su tallafa wa wadanda aka tura can idan wasu ‘yan ta’adda suka sake kai farmaki, Daily Nigerian ta wallafa.

Elkanah ya yaba da jajircewar jami’an tsaron a kan yadda suka zage damtse suka yaki ‘yan ta’addan kuma suka ci gaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin jama’an jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here