Ba Zamu Cigaba Da Barin ‘Yan sanda Su na Mutu a Hannun ‘Yan Ta’adda ba – Johnson Kokumo

Ba za ta sabu ba, kare ya kashe ragon layya, cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo.

A cewarsa, babu dan sandan da zai sake bari dan ta’adda ya cutar da shi.

Ya ce ba zai bar dan ta’adda mai rike da wuka, ya kashe dan sanda mai AK-47 ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, Johnson Kokumo, ya ce ‘yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannu ‘yan ta’adda su na kashesu kamar kaji ba.

A ranar Litinin, Kokumo ya fadi hakan a wani taro na kaddamar da kungiyar ‘yan sa kai 70 a karamar hukumar Ikopaba-Okha da ke jihar.

Ya bayyana asalin manufar zanga-zangar EndSARS, inda yace dan sa ya kashe kansa bayan masu zanga-zangar sun janyo masa asarar naira miliyan 7.

A cewarsa, kamata yayi a ce ‘yan sanda sun yi amfani da makamai wurin kare rayuwarsu da ta wasu mutane, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ya ce za su cigaba da fadi wa ‘yan sanda cewa kada su yi zalunci, amma kada su kuskura su bari wani dan ta’adda mai wuka ya kashe dan sanda mai AK-47.

Ya kara da cewa, “Yan sanda ba za su tsaya su mutu a hannun ‘yan ta’adda ba.Kuma ina so kowa ya sanar da makwabtansa da yaransa wannan sakon.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here