‘Yan Sanda Sunyi Nasarar Kama Wani Dan Ta’adda

‘Yan sandan jihar Rivers sun samu nasarar damkar wani dan ta’adda tare da yaransa.

Mutumin ya addabi fasinjojin jiragen ruwan bakin kogin Bonny, da ke Port Harcourt.

Sakamakon harin da suka kai ranar Alhamis, sun ji wa fasinjoji raunuka har da kashe wani.

Wani dan ta’adda wanda ya addabi fasinjojin jiragen ruwan kogin Bonny da ke Port Harcourt a jihar Rivers, Dan Ezekiel George, ya shiga hannun ‘yan sanda, tare da yaransa bayan sun kai wa wasu fasinjoji hari, har wani mutum ya rasa ransa.

Wanda ake zargin, mai shekaru 28 dan asalin Asarama ne da ke karamar hukumar Andoni a jihar Rivers.

‘Yan ta’addan sun yi awon gaba da kayan matafiyan a ranar Alhamis da safe, The Punch ta ruwaito.

Wani mutum, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar wa da manema labarai cewa fasinjoji da dama sun samu mugayen raunuka sakamakon adduna da wukaken da ‘yan daban suka yi amfani da su, har wani ya rasa ransa.

Bayan tuntubar kakakin hukumar ‘yan sandan yankin, Nnamdi Omoni, ya ce wasu sun zo hannu, amma har yanzu suna farautar wani gawurtaccen ‘dan ta’adda.

Omoni ya ce, “Zan iya tabbatar da aukuwar lamarin, don ya faru ne a kogin Bonny. Daniel Clifford George daga Asarama da ke karamar hukumar Andoni, yana daya daga cikin wadanda ‘yan sanda suke nema ruwa a jallo. Kuma sun samu nasarar damkarsa tare da abokan tarayyarsa.”

Ya tabbatar da cewa Daniel ne shugaban ‘yan ta’addan, kuma yanzu haka sun fara tambayarsa don binciko sauran ‘yan ta’addan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here