‘Yan Bindiga: Rundunar ‘Yan Sanda ta yi Nasarar Kama Wani Mai Unguwa da Wasu Mutane

 

Mai unguwar ƙauyen Tungan-Iliya da wasu mutane goma sun shiga hannu bisa zarginsu da kai hari a ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar Neja.

Rundunar yan sanda ta ce ta na ƙara faɗaɗa bincikenta don ganin an kamo tare da gabatar da sauran masu laifin a gaban kotu domin yi musu hukuncin da ya dace.

Jihar Neja na fuskantar karuwar hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Rundunar yan sanda ta jihar Niger, ta yi nasarar cafke mai unguwar ƙauyen Tungan-Iliya da wasu mutane goma bisa zarginsu da kai hari a ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana haka inda ya ce sun samu nasara ne biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu inda suka kai samame a maɓoyar maharan dake dajin Tunga-iliya.

Da ya ke zantawa da manema labarai Wasiu ya ce, “Dakarun mu sun yi musayar wuta da su inda aka kama bakwai cikin su, biyar kuma sun ji mummunan rauni.

“Cikin waɗanda ake zargi harda mai unguwar kauyen Tunga-iliya da Sumayya Bello wacce take kaiwa yan ta’addan bayanai.”

Mr Abiodun ya ce, rundunar yan sanda na ƙara faɗaɗa binciken ta don ganin an kamo tare da gabatar da su gaban kotu domin yi musu hukuncin da ya dace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here