‘Yan Sanda 7 Sun Rasa Rayukansu a Harin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Ofishin ‘Yan Sanda a Yankin Kudu

 

‘Yan bindiga da suke kaiwa ‘yan sanda da ofisoshinsu hari sun sauya salo a inda suka koma yankin kudu-kudu na kasar nan.

A cikin sa’o’i kadan, an kaiwa ofishin ‘yan sanda hari kuma an kashe jami’ai a jahohin Ribas da na Akwa Ibom.

Yayin da ake tunanin ‘yan sanda 7 sun mutu a harin Ribas, an kashe wasu jami’ai shida a harin da aka kai Akwa Ibom.

‘Yan bindiga da ake zargin mambobin IPOB ne sun kai mugun farmaki ofishin ‘yan sanda dake Odoro Ikpe a karamar hukumar Ini ta jahar Akwa Ibom.

Jami’ai shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai a sa’o’in farko na ranar Asabar, 8 ga watan Mayu, The Punch ta ruwaito haka.

Hakazalika, a yayin bada rahoton harin, The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da ake kai hari cikin mako daya a jahar ta kudu.

Legit.ng ta tabbatar da cewa wannan harin ya zo ne yayin da ake ta kai hare-hare ofishin ‘yan sanda a yankin.

Hare-haren ‘yan bindiga ya zama ruwan dare domin kuwa ba a yin kwanaki kalilan ba tare da sun kai mugun hari ba.

Suna kone ofishin ‘yan sanda tare da kashe jami’ai. Duk da ana zargin mambobin IPOB da kai miyagun hare-hare, su kan musanta hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here