‘Yan Sandan Katsina Sunyi Nasarar Kama Wasu ‘Yan Fashi

‘Ƴan sanda a Jihar Katsina sun cafke wasu matasa da ke kashe ƴan acaɓa bayan sun sace baburansu.

Asirin matasan ya tonu ne yayin da ake bincike kan fasa wani shago da aka yi sannan aka yi sata.

Yayin amsa tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun kashe wani matashi sun sace babur ɗinsa an tafi da babur ɗin Nijar Rundunar.

Ƴan sanda Jihar Katsina ta kama ƴan kungiyar fashi da suke ƙware wurin kashe masu acaɓa bayan sun ƙwace babur ɗin su.

Kakakin ƴan sandan jihar DSP Isah Gambo ne ya gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Ya ce sunayensu sun haɗa da Surajo Lawal Na Kofar Guga Quarters, Hamisu Sama’ila da aka yi wa inkiya da Abu Kwalwa, da Habila Abubakar duk mazauna Sabon Gida Quarters a Katsina.

Ya ce dubunsu ya cika ne yayin da aka kama su a ranar 16 ga watan Nuwamba misalin ƙarfe 8 na dare yayin da ake binciken zargin fasa shago da sata.

“A yayin binciken wadanda ake zargin sun amsa cewa a ranar 14/11/2020 misalin ƙarfe 11 na dare, sun haɗa baki sun tare wani ɗan acaɓa, Yusuf Isiya mazaunin Farin Yaro Quarters a Ring Road Katsina suka kai masa hari da muggan makamai suka kashe shi suka tafi da babur ɗinsa ƙirar Hero da kudinsa ya kai Naira dubu ɗari da hamsin (N150,000:00K)”, in ji Gambo.

“Har wa yau, wadanda ake zargin sun ce wani Anas Gagare, 25 da Danfakal, 26, (da ake kan nema) sun kai babur ɗin Maraɗi a Jamhuriyar Nijar. Ana cigaba da bincike,” ya ƙara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here