Kano: Yan sanda Sun Kama Wasu Mutane yayin zanga-zangar EndSARS

Jami’an yan sandan Kano sun kama mutane 55 a yayin zanga-zangar EndSARS a jihar

An kama mutanen kan zarginsu da ake yi da hannu wajen tayar da zaune-tsaye a unguwar Sabon Gari – Rahoton ya kuma bayyana cewa an same su dauke da muggan makamai tare da fasa shagunan mutane da yi masu sata Rundunar yan sanda ta jihar Kano, ta tabbatar da kama mutane 55 bisa zarginsu da ake da hannu wajen tayar da kayar baya a unguwar Sabon Gari da ke birnin jihar, a yayin zanga-zangar EndSARS. Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema Labarai a yau Lahadi, 25 ga watan Oktoba. Kiyawa ya bayyana cewa an damke mutanen ne, saboda kama su da aka yi dauke da makamai da suka hada da adduna, wukake, gorori da kuma bindigogi.

Har ila yau an kama su da laifin fasa shagunan mutane tare da debe kayayyakin da ba nasu ba, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Kakakin yan sandan ya kuma jinjinawa al’ umman Kano a kan irin hadin kai da suka ba rundunar wajen zakulo bata garin.
Ya kuma ce rundunar ’yan sanda ta jihar ba za ta lamunci duk wasu ayyukan ta’addanci da zanga-zangar da ta wuce gona da iri ba, domin a cewarsa rundunar a shirye ta ke wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here