Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Katsina ta Kama ‘Yan Damfara Uku

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Katsina ta samu nasarar cafke wasu yan damfara su uku.

Yan damfaran na kiran mutane a waya su basu tsoro da cewa su aljanu ne su biya kuɗi ko su kashe wani nasu.

Mai magana da yawun yan sandan jahar ya bayyana cewa sun kama su ne bayan sunyi makamancin haka ga wata mata.

Rundunar ‘yan sanda a jahar Katsina sun cafke wasu mutane uku ‘yan damfara waɗan da ke damfarar mutane da sunan cewa su aljanu ne.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya bayyana sunayen mutanen; Usman Adamu, 40, Abba Ibrahim, 38, da kuma Abdurrauf Iliyasu, 39.

SP Gambo yace an sami nasarar kama waɗan da ake zargin ne bayan sun kira wata mata mai suna Jamila Sulaiman a waya sun umarce ta da taje kan hanyar fita garin Yar Gamji ta aje kuɗi N150,000.

Sun tsorata matar da cewa su “aljanu” ne idan kuma batayi abinda suka saka ta ba to zasu saka rayuwar mahaifanta ko kuma ‘yayanta a cikin hatsari ko su kashe su.

Matar ta tsorata matuƙa, hakan tasa ta ɗauki maƙudan kuɗaɗen da suka buƙata taje ta aje musu a inda suka ce. Sannan kuma ta tura musu N97,000 a bankin ɗaya daga cikinsu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A lokacin da yan sanda suka fara bincike “Mun bibiyesu kuma muka kama su” kuma sun amsa laifin su dama waɗansu laifukan daban “Muna cigaba da bincike” inji shi.

Rundunar yan sandan ta kuma ce ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne; Hassan Magu, 20, da Salisu Lado, 25.

An kama mutanen biyu ya yin da suke kan hanyar su ta zuwa yankin karamar hukumar Ɗan-dume domin kai hari.

SP Gambo Isa ya ce mutanen biyu sun amsa laifin su kuma sun ce suna daga cikin waɗan da ke aiki a yankunan jahohin Katsina, Zamfara da kuma Kaduna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here