‘Yan Ta’adda Sun Aika Kasurgurmin ‘Dan Bindiga Lahira a Jihar Zamfara

 

Jihar Zamfara – Rikici ya balle tsakanin dabar Gurgun Daji da wata dabar daban, wanda ya jawo hallaka daya daga cikin jagororin yan ta’adda da su ka addabi mazauna Zamfara da kewaye.

Rahotanni sun bayyana cewa an tarfa jagoran yan ta’adda Kachalla Ibrahim Gurgun Daji, a Kwanar Nasiru da ke Mada a karamar hukumar Gusau.

Jaridar Zagazola ta tattaro cewa wata dabar yan ta’adda ta kashe Kachalla Ibrahim Gurgun a ranar Lahadi bayan kazamar arangama.

Yadda Kachalla ya addabi mazauna Zamfara

An zargi jagoran yan ta’adda Ibrahim Gurgun Daji da gallazawa matafiya da sauran mazauna hanyar Kwatarkwashi-Mada da kewaye.

An gano cewa ya kitsa miyagun ayyukansa ne daga kauyen Shangel da ke kauyen Mada, inda ya gawurta wajen satar mutane har cikin garin Gusau.

Yadda Kachalla Gurgun Daji ya boye yan bindiga

An gano yadda dan ta’adda, Kachalla Ibrahim Gurgun Daji ya rika ba sauran miyagun yan ta’adda da sauran bata-garin jama’a mafaka ciki har da Bello Taggoje.

Kisan Kachalla Ibrahim Gurgun Daji zai kara bunkasa yakin da sojojin yan kasar nan ke yi da yaki da ta’addanci a fadin kasar nan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here