‘Yan Ta’addan na Hira da Gidajen Rediyo da Jaridu Cikin Harshen Hausa, Amma Har Yanzu ba su San Yadda Hukumomi za su Kama su ba – Shehu Sani

 

Tsohon dan majalisar dokoki daga Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana sunayen wasu jagororin ta’addanci da aikata barna a yankin Arewa.

Sani ya yi zargin cewa sunayen ‘yan ta’addan sun kusa cike gidajen ‘yan Arewa, inda ya ce suna yawo cikin walwala ba tare da tsangwama ba.

Fitaccen dan siyasar ya kuma lura da cewa, ‘yan ta’addan na hira da gidajen rediyo da jaridu cikin harshen Hausa.

Shehu Sani ya bayyana sunayen manyan ‘yan ta’adda a yankin Arewa da ake zargin su ne ke yawo cikin walwala da aiwatar da hare-haren ta’addanci a yankin.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon sanatan daga Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris.

Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8 ya bayyana sunayen manyan shugabannin ta’addancin Arewa kamar su Bello Turji, Dogo Gide, Manjagara, da Baleri.

Ya kuma yi mamakin yadda wasu jagororin ta’addanci a Arewa, wadanda suka kusan sunayensu suka zama sanannu gidaje ke ci gaba da yawo kana hukumomi suka gagara kama su.

A cewarsa, wadanda ake zargin shugabannin ‘yan ta’adda ne, amma kuma suke samun damar hira da gidajen rediyo da jaridu cikin harshen Hausa.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Bello Turji, Dogo Gide, Manjagara da Balleri sune gawurtattun jagororin ‘yan ta’adda na Arewa wadanda suka yi hira da gidajen rediyo da jaridu a cikin harshenmu na Hausa, amma har yanzu ba su san yadda hukumomi za su kama su ba. Ni dai ban gane ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here