‘Yan Uwa Sunyi Sanadiyyar Hallaka ‘Dan Uwansu a Jahar Imo

 

‘Yanuwa sun hada-kai sun hallaka ‘Danuwansa saboda sabanin rabon gado a Imo.

Wani ‘danuwan mamacin ya rankwala masa karfe, hakan ya yi sanadin cikawarsa.

Ko da aka gaggauta aka kai Bawan Allah zuwa asibiti a Okuku, sai aka ji ya rasu A ranar Talata wata musiba ta auku a Okuku, garin Owerri da ke jahar Imo inda wasu ‘yan gida daya su ka bugi babban yayansu, har ya bar Duniya.

Punch ta fitar da rahoto cewa ‘yanuwan jini sun kashe Chinonso Azuatalam ne a dalilin sabanin da su ka samu wajen raba dukiyar mahaifinsu da ya mutu.

Chinonso Azuatalam wanda aka fi sani da Dakwada ya mutu ya bar iyalinsa da ciki a sakamakon mummunan bugun da ‘yanuwansa su ka yi masa.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa marigayin duka ne a gaban ‘yanuwan mahaifiyarsa wadanda su ka zo su karbi gadon da ake rikici a kansa.

Wata majiya ta ce marigayin ya na fada da kaninsa mai suna Chibuzor, sai ‘danuwan na sa na jini ya rankwala masa wani karfe a keya, nan-take ya kife.

An garzaya da Chinonso zuwa wani asibiti, inda ana isa aka tabbatar cewa ba ya numfashi.

Bayan ‘yanuwan mamacin sun samu labarin ya cika, sai su kayi maza, su ka tsere. Chibuzor wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘danuwansa, tagwaye ne.

Bayan nan, wata ‘yaruwar marigayin, Chioma Azuatalam, wanda jami’ar ‘yan sanda ce ta yi wa mai dakin Chinonso mai dauke da juna biyu mugun duka.

Shugaban mutanen kauyen Okuku, Martin Daniel, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya ce an kama ‘yaruwar mamacin da ta yi wa matarsa dukan.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Imo, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da cewa Chioma da daya daga cikin ‘danuwan mamacin sun shiga hannunsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here