‘Yan Wasan Kwallon Kafa 22 Sun Rasa Rayukansu a Hatsarin Mota a Malawi

Akalla ‘yan wasan kwallon kafa 22 da magoya bayan kungiyarsu sun mutu a gundumar Karonga da ke arewacin Malawi, bayan da motar da suke ciki ta kife a lokacin da suke dawowa daga wani wasa.

Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta ce motar da ke dauke da mutane kusan 80 ta juye a daren ranar Asabar bayan da direban ya kasa nade kan motar yadda ya kamata, sai ya doki wani shingen da ke gefen hagu na titin.

An kai wasu fasinjoji da dama asibiti – kuma akalla 12 daga cikinsu sun sami munanan raunuka.

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da yin umurni ga sashen kula da bala’o’i da su bayar da gudunmuwa cikin gaggawa ga dukkan iyalan wadanda abin ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com