BAMU YARDA BA; GINA 360 A DAKATA!!!

Gabatarwa;

Kasancewar mu Hausa/Fulani, tabbas muna da al’ada hadi da Addini wadanda suke kyamatar irin duk wani nau’in Ash-sha, wanda ya saba da duka biyu (Al’ada da Addini), ko kuma daya daga cikinsu (Addini ko Al’ada).

Unguwar dakata, daya ce daga cikin unguwanni masu tarihi a karamar Hukumar Nasarawa, haka mafi yawan mazauna cikinta Muslamai ne, wadanda suke kare Al’adarsu ta Hausa Fulani dakuma koyarwar Addinin Muslinci.

MENE NE 360?;

Wani Gidan Shar holiya ne, Gidan rawa ne, wanda za’a iya kiransa da Night Club, Gidan Gala, dss. Misalinsa kamar; Eleganty dake Airforce Base, ko Bubble Plus, inner circle dake kan Airforce base by Jaba Road(kowa yasan me ake agurin).

Amman Suna fakewa da Restaurant ne! Gaskiya ba haka bane domin idan muka duba 360 dake kan titin Hadejia Road, da Piccolo dake Tukur Road, Race course, kano; wanda mallakin mutun daya ne.

Bisa ka’ida, idan dai anbi maslahar mu Mutanen yanki, to tabbas wannan guri ba’a bukatarsa a wannan yanki, meyasa bazasu nemi wuri irin wadancen kamarsu Tukur Road, Ahmad bello, Hadejia Road?

MAKOMAR MUTANEN DAKATA

Tabbas Gina 360 a dakata ba karamin barazana bane da tarbiyar Yan dakata, kuma shine tushe da duk wani mai irin tunanin zaizo yasake bude wani Abu makamancin 360, koma wanda yafi shi.

JAN KUNNE

Muna kira ga mahukunta; hakimin Nasarawa, Dagacin Dakata, Masu unguwannin dakata, Hisba Command Nasarawa, Dakata Police Station, Malamai da limaman Juma’a na Dakata, da duk wasu wanda suke da ikon fada aji, su fito suhana wannan Wuri wanzuwa.

Sameen Y Saeed (Dr.SYS)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here