Abdulaziz Yari ya Bar Hannun Hukumar EFCC

Sababbin bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa Alhaji Abdulaziz Yari ya bar hannun EFCC.

‘Yanuwan tsohon Gwamnan sun shaidawa manema labarai cewa ya dawo gida a ranar Alhamis.

Hukumar EFCC ta ce ta ba Ahmed Idris beli, ana binciken Akanta Janar din ne da taba Baitul-mali.

Abuja – Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta saki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

‘Yanuwa da dangin Alhaji Abdulaziz Yari ne suka shaidawa jaridar nan ta Daily Nigerian wannan labarin a yau, ranar Juma’a, 6 ga watan Maris 2022.

Kamar yadda na-kusa da tsohon gwamnan suka tabbatarwa manema labarai, an saki Yari ne a jiya.

Idan za a tuna, jami’an EFCC sun yi ram da tsohon gwamnan na Zamfara a gidansa a unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja a makon nan.

Kashin da ke jikin Yari Ana zargin akwai hannun Yari a badakalar da ake tuhumar Ahmed Idris da tafkawa na akalla Naira biliyan 84 a lokacin da yake kujerar Akanta Janar.

Jaridar ta ce an kama ‘dan siyasar ne tare da babban darektan kamfanin Finex Professional.

Idan zargin da ake yi ya tabbata, Yari ya amfana da Naira biliyan 22 daga cikin Naira biliyan 84 da ake tunani AGF din ya karkatar daga baitul-mali.

Zargin shi ne Yari wanda shi jam’iyyar APC ta ba takarar kujerar Sanatan yammacin Zamfara ya amfana da kudin ta kamfanin Finex Professional.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here