Yawan Falasɗinawan da aka Kashe a Gaza
Ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta wallafa sabuwar ƙididdigar mutanen da suka mutu a Zirin tun bayan ɓarkewar yaƙi.
Aƙalla mutum 24,100 ne aka tabbatar da mutuwarsu, a cewar ta. Ta ƙara da cewa fiye da mutum 100 aka kashe cikin sa’a 24 da ta gabata.
Read Also:
Sashen BBC Verify da ke tabbatar da sahihancin labarai a baya ya duba yadda ake ƙirga mutanen da suka mutu a Gaza.
Yaƙi ya ɓarke ranar 7 ga watan Oktoba bayan da Hamas ta kai hari kan Isra’ila tare da kashe mutum 1,200 da garkuwa da ɗaruruwa.
Tun lokacin kuma Isra’ila take kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a wani mataki na martani – ban da tsagaitar wutar da aka samu na tsawon mako ɗaya.