Allah ya yi wa Yayan Marigayiya Mama Taraba, Sanata Abdulazeez Rasuwa
Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, yayan tsohuwar ministar mata, marigayiya Hajiya Aisha Jummai, rasuwa.
Abdulazeez ya rasu ne a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin ya wakilci yankin Taraba ta Tsakiya a tsakanin 1999 zuwa 2007.
Tsohon sanata Abubakar Abdulazeez Ibrahim wanda ya kasance yayan marigayiya Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Mama Taraba), ya rasu.
Read Also:
Marigayin mai shekaru 64 wanda ya rasu a gidansa da ke Jalingo a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, bayan gajeriyar rashin lafiya ya wakilci yankin Taraba ta Tsakiya a tsakanin 1999 zuwa 2007.
Bugu da kari, marigayi Ibrahim ya yi takarar kujerar gwamna a jahar sau biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya yi karatun Injiniya da Gudanar da Kasuwanci a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, jahar Kaduna, kuma shine mamallaki Makarantun Firamare da Sakandare na Ibramiyya da Kwalejin Ilimi ta Peacock a Jalingo.
Kamar yadda yake bisa koyarwar addinin Musulunci, za a yi jana’izar marigayin da karfe 1:30 na rana a fadar mai martaba sarkin Muri.
Sannan daga bisani za a binne shi a makabartar Jika da Fari, inda aka binne marigayiya ‘yar uwarsa, Sahara Reporters ta rahoto.