Young Boys Sun ci Manchester United 2-1 a Gasar Champions League

 

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 136 a gasar Champions League a wasan da Young Boys ta ci Manchester United 2-1 ranar Talata.

Ronaldo ne ya fara cin kwallo minti 13 da fara tamaula, inda Young Boys ta farke ta hannun Nicolas Moumi Ngamaleu a wasan na rukuni na shida.

Daf da za a tashi Young Boys ta kara na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu da hakan ya sa ta hada maki uku a karawar.

A wasa 68 da ya buga a Champions League tun bayan da ya cika shekara 30 da haihuwa, Ronaldo ya ci kwallo 63, jumulla yana da 136 a raga.

Hakan ya sa yana kan gaba da tazarar 35 tsakanin ‘yan wasan da suka kai shekara 30 ko fiye da haka da suka ci kwallo a tarihin Champions League.

Lionel Messi dan kwallon Paris St Germain shine na biyu a yawan cin kwallaye a Champions League mai 120 a raga.

United ta karasa karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Wan Bissaka jan kati.

Aaron Wan-Bissaka shine dan wasan Manchester United na farko da aka bai wa jan kati a Champions League tun bayan wanda aka kori Nani a fafatawa da Real Madrid cikin Maris din 2013.

An buga karawar da ‘yan kallo a karon farko a gasar tun bayan 2020, sakamakon bullar cutar corona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here