Ina Iya Zama Shugaban Majalisar Dattawa Nan Gaba – Bashir Machina

Ɗan takarar Sanata a Yobe ta Arewa karkashin jam’iyyar APC, Bashir Sheriff Machina, ya ce yana iya zama shugaban majalisar dattawa nan gaba.

A wata hira da jaridar Najeriya ta Leadership ta yi da shi, ɗan takarar ya ce mutane na ta tuntubarsa da sunan ya janyewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, amma hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Tana dai ƙasa tana dabo game da makomar siyasar shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmed Lawan, bayan ya rasa takarar shugaban ƙasa a APC da ya nema, wanda Bola Tinubu ya lashe.

Kuma shekarunsa 15 yana rike da kujerar Sanata a Yobe ta Arewa.

Abin da Machina ke cewa

A tattaunawarsa da BBC, Bashir Machina, ya ce ya fitar da takarda a shafukan sada zumunta wanda ya aikewa jam’iyya, kan tuntubar da aka yi ma sa ko yana nan kan takararsa.

Ya ce shi kuma ya amsa da cewa bai janye ba, kuma yana kan takararsa. Sannan ya ce shi baki da baki Ahmed Lawan bai tuntube shi ba, don haka yana nan kan bakarsa kamar yada jama’a suka zaɓe shi.

Dan takarar ya kuma ce “ko da an tuntube ni ma ba zan janye takarata ba, saboda mutane ne suka zabe ni a zaben fitar da gwani domin na wakilce su.

An kada kuri’a an tantace na yi nasara, don haka duk bayanan da ake yadawa cewa na janye ko zan janye labaran boge ne”, in ji ɗan takarar.

Bashir ya kuma ce yana kan bakarsa, kuma yana da tabbacin nasara, saboda manufar takararsa ita ce jagoranci nagari, saboda jama’a su samu wakilci na gari.

Akwai “tsare-tsaren da nake son aiwatarwa saboda a shirye nake, na yi kintsawar da zan kasance wakili nagari ga jama’ata”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here