Kasar Zambia ta Bayyana Cewa Zata Taimakawa Najeriya Wajen Magance Matsalar Tsaro 
Kasar Zambia ta bayyana niyyar taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaro.
 Jakadan Kasar ya bayyana cewa Zambia na da ilimi wajen kawar da matsalar tsaro.
 Najeriya na fama da matsalar tsaro da ta addabi sassa daga Kudu zuwa Arewa.
Abuja – Gwamnatin kasar Zambia a ranar Talata ta bayyana damuwarta kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya kuma ta yi alkawarin cewa zata taimakawa Najeriya wajen maganceta.
Kasar Zambia ta ce zata taimakawa Najeriya ne saboda ita ma ta taka rawar gani wajen samun yancin kasashen kudancin nahiyar Afrika daga turawan mulkin mallaka.
Jakadan Zambia dake Najeriya, Solomon Samuel Jere, ya bayyana hakan yayin sanar da taron zaman lafiyan da Cocin Seventh Day Adventist suka shirya yi ranar Asabar mai zuwa, rahoton Punch.
Yace Zambia shirya take da taya Najeriya da labaran leken asiri wanda zasu taimaka wajen samar da tsaro.
Yace:
“Zambia ba zata zuba ido ‘yan uwanta dake Najeriya su cigaba da fama da ta’addanci ba. Ku san yanzu Zambia tayi sabon Shugaba wanda ya samar da sabbin hanyoyi.”
“Yanzu haka, akwai kasashe da dama irinsu India da wasu kasashen Afrika dake Zambia muna horar da jami’ansu wajen yaki da ta’addanci da yan bindiga.”
“Saboda haka, Zambia zata taimakawa Najeriya wajen yaki da yan ta’adda.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here