Yaki da ‘Yan Ta’adda: Gwamnatin Zamfara Za ta Farfado da Rundunar Yan sa kai a Jahar

 

Gwamnatin jahar Zamfara zata farfado da rundunar tsaron farar hula ta hadin gwiwa (CJTF) wacce aka fi sani da “Yan sa kai”.

Gwamnatin za ta farfado da rundunar ne don yaki da ‘yan ta’addan jahar kamar yadda shugaban kwamitin tsaron jahar ya bayyana.

Abdullahi Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Gusau yayin tattaunawa da manema labarai.

Jahar Zamfara – Gwamnatin jahar Zamfara za ta farfado da kungiyar hadin gwiwa ta tsaro na farar hula ta CJTF wacce aka fi sani da “Yan sa kai” don kawo tallafi ga jami’an tsaron jahar akan ‘yan ta’addan da suka addabi Zamfara, rahoton Premium Times.

Shugaban kwamitin tsaro da yanke hukunci ga ‘yan bindiga na jahar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da NAN tayi da shi a ranar Talata.

Gwamnatin jahar ta yanke shawarar ne don kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da ke jahar

Kamar yadda Premium Times ta rawaito, Shinkafi, wanda shi ne mai bai wa gwamna Bello Matawalle shawarwari a harkar gwamnati ne ya ce:

“Gwamnatin jahar ta yanke wannan shawarar ne bisa ganin yadda ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane suke ci gaba da yawaita a fadin jahar.

“Gwamnatin za ta yi hakan bisa wani sabon sharadi. Wajibi ne duk mai neman shiga kungiyar ‘Yan sa kai’ zai gabatar da mutane 3 su kasance tsayayyu a gare shi kafin a jaddada shi.”

“Za a farfado da rundunar Yan sa kai don taimako ga jami’an tsaro wurin ganin karshen duk wasu ‘yan bindiga da masu basu bayanai.”

Premium Times ta rawaito yadda Shinkafi ya nemi taimakon rundunar don yaki da rashin tsaro a fadin jahar.

Shinkafi ya yaba wa mazauna jahar akan juriyar su

“Mun yaba wa mazauna jahar bisa hakuri, addu’o’i, juriya da karfin guiwar da suke bayarwa ga sababbin dokokin tsaron da jihar ta kafa don kawo karshen ta’addanci da garkuwa da mutane.

“Yanzu haka jami’an tsaro sun samu tarin nasarori sakamakon luguden wutar da sojin kasa da na sama suke yi wa ‘yan ta’adda,” a cewarsa.

Mai bai wa gwamnan shawara ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ta dakatar da hanyoyin sadarwa a jahar Zamfara da sauran hanyoyin tallafa wa tsaro duk don kakkabo duk wasu ‘yan ta’adda a jahar Zamfara.

“Rufe kasuwannin shanu ma tana daya daga cikin matakan da gwamnatin jahar ta dauka sakamakon yadda ‘yan ta’addan suke kasuwancin miyagun makamai da shanu,” kamar yadda ya ce.

Shinkafi ya yaba wa Gwamna Matawalle akan sababbin hanyoyin da gwamnatin sa ta dauka don yaki da duk wasu ta’addanci a jahar.

A cewar sa, yanzu haka jami’an tsaro sun ragargaji ‘yan ta’adda da dama da ke fadin jahar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here