Gwamnatin Zamfara ta Rufe Makarantun Jahar

 

Gwamnatin jahar Zamfara ta sanya dokar ta baci a fadin kananan hukumomi 14 dake jahar.

Hakazalika gwamnatin ta kulle dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake dukkan kananan hukumomin jahar.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai garin Kaya, karamar hukumar Maradun ta jahar da dafiyar Laraba inda suka yi awon gaba da daliban makaranta.

A cewar TVCNews, dokar ta bacin zata kama ne daga daga karfe takwas na dare zuwa bakwai na safe.

Rahoton tace:

“A cewar gwamnatin jahar, an dauki wannan mataki ne domin dakile hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jahar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here