Sarkin Zazzau ya Nada Sabon Ciroman Zazzau

 

Ba tare da bata lokaci ba, an nada sabon Ciroman Zazzau.

Har yanzu, sabon Sarkin Zazzau na cigaba da fuskantar kalubale daga cikin ‘yan majalisarsa.

Hakan ya sa ta kwancewa daya daga cikinsu rawani a makon nan Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi karin girma ga Mallam Shehu Tijjani Alu Dan Sidi Barden Zazzau zuwa Ciroman Zazzau.

Wannan ya biyo bayan kwance rawanin tsohon Ciroman Zazzau, Alhaji Sai’du Mai Lafiya. Sarkin ya tube rawanin Ciroman Zazzau ne saboda zargin rashin biyayya da girmama masarautar.
A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2020, Ahmed Nuhu Bamalli ya gaji Alhaji Shehu Idris a kan karagar Sarkin Zazzau.

Cikin yan watannin da yayi kan karagar mulki, an samu sauye-sauye da dama a masarautar Zazzau Ga kadan daga cikin sauye-sauyen:

1. Yi wa gidan Bare-bari babban nadi.

2. Karbe sarautar Iyan Zazzau daga gidan Katsinawa zuwa na gidan Abbas Tajuddeen na Mallawa.

3.Magajin Garin Zazzau Sabon sarki ya bada sarautarsa ta Magajin Gari ga ‘danuwansa, Mansur Nuhu Bamalli.

Mai martaba ya tsallake mai bi masa a gidan Nuhu Bamalli, ya dauko Barde Kerarriya.

4. Maye gurbin wadanda suka rasu Bayan Iyan Zazzau, Ahmed Bamalli ya nada sababbin Sa’i da Talban Zazzau bayan rasuwar wadanda su ke rike da wannan mukamai.

Talba ya koma gidan Iya Bashar Aminu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here