ALLAH ya yi wa Farfesa Ɗahiru Yahaya Rasuwa

 

Allah ya yi wa fitaccen masanin tarihi, Farfesa Ɗahiru Yahaya rasuwa a jahar Kano.

Marigayin ya rasu ne a a yau Laraba a asibiti bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ɗan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa ya kuma ce za ayi jana’izarsa a Ungogo, Kano Shararren farfesan Tarihi dan asalin jahar Kano, Ɗahiru Yahaya ya riga mu gidan gaskiya.

Dahiru Yahaya ya rasu yana da shekaru 75 a duniya, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kafin rasuwarsa ya koyar a jami’ar Bayero ta Kano da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Ya rasu ne a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekarar 2021 a wani asibiti bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Ɗan uwan marigayin malamin jami’an, Bashir Habib Yahaya, ya tabbatar wa manema labarai rasuwarsa.

Ya kuma ce za a yi wa marigayin jana’iza a gidansa da ke Ungogo a jahar Kano misalin ƙarfe 4 na yamma.

Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata uku, yara ashirin-da-biyu da jikoki masu yawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here