By Adam Muhammad
Hakika zaben Gwamnan Kano a 2019 zabe ne da zai zo na rashin tabbas gurin waye zai iya lashe zaben ba tare da wata tangarda ba, sakamakon yan takara da ake da su a jam’iyyu mabamban ta kamar haka:
APC: Ita ce jam’iyya mai mulki tun daga kan shugaban kasa har zuwa gwamnan Kano mai ci a yanzu wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kasancewar jam’iyyar tana da dimbin magoya baya da farin jinin al’umma a shekarar 2015 inda ta lashe zabe da mafi yawan rinjaye a mafi yawancin jihohin arewacin Najeriya, ciki har da nan Kano, sai dai kuma jam’iyyar ita ma a yanzu tana fama da rikicin cikin gida a inda tun daga farko ta fara rasa manayan yan siyasa irin su Engr. Rabiu Kwankwaso da sauran su.
Babban Nakasun da jam’iyyar za ta samu shine na faifan bidiyon da yake zagawa a yanzu inda ake nuna wani mutum yana karbar daloli yana zubawa a aljihu a matsayin karbar na goro wanda ake alakanta wannan mutumin da Dr. Abdullahi Umar Ganduje wato Dan takarar Gwamna a karkashin tutar jam’iyyar APC, wannan abu zaiyi tasiri sosai a wurin jama’a masu kada kuri’a, ta yadda idan har Wannan Dan Takara baiyi saurin wanke kansa daga wannan zargi da ake masa ba to wannan bidiyon zaiyi tasiri a wurin jama’ar jihar Kano.
PDP: Jam’iyya ce da ta mulki kasar Najeriya tsawon Shekarau 16, kuma jam’iyya ce mai karfi a wannan kasa inda suka tsaida Dan takarar su wato Abba Kabir Yusif surikin Rabiu Kwankwaso, wanda shine yayi mashi kwamishina na Ayyuka a lokacin mulkin Kwankwason karo na biyu. Kwankwason wanda yayi gwamna har sau biyu a Kano kuma yana da dimbin magoya baya a Kano masu bin Darikar Kwankwasiyya.
Babban Nakasun da jam’iyyar za ta samu shine na bakin jinin da jam’iyyar ta dauko tun daga lokacin mulkin Goodluck Ebele inda mafi yawancin jama’ar Arewacin Najeriya suke mata Kallon jam’iyyar da tayi sake wajen yakar yan Boko Haram, Sannan Babban nakasun da zai sami jam’iyyar shine na ganin manufar wannan Dan takara shine cewa ba zai ci Amanar Kwankwaso ba.
Read Also:
Haka zalika wajen zaben fidda gwani na Dan takarar Gwamna jam’iyyar tayi karfa karfa inda ta bawa Kwankwason kai da fata na ya fitar da duk Dan takarar da yake so, bayan ya dawo jam’iyyar ya tarar da mutane sama da mutum 100 sun sayi foma fomai na yin takara daban daban, amma jam’iyyar tayi fatali da su ta kawo wadanda Kwankwason yake so, wannan ta sa jam’iyyar ta rasa magoya baya da yawa a jihar Kano ciki har da manyan yan takarar Gwamna mutum shida.
PRP: Jam’iyya ce wadda Mallam Aminu Kano ya kafa ta domin ceton Talakawa, jam’iyyar ta samu karbuwa tun a wancan lokacin inda ta kafa Gwamna a wannan jihar ta Kano, anyi yunkurin dawo da ita a lokuta daban daban amma hakan su bai cimma ruwa ba.
A wannan lokacin ma jam’iyyar tana nan da ranta inda ta dauko Dan takarar Gwamna wanda yayi takara 2011 da 2015 wato Mallam Salihu Sagir Takai, Takai dai yayi Shugaban Karamar hukumar Takai a shekarar 1999 inda jama’ar garin suka shaida ba a taba shugaban da suka mora kamar sa ba, sannan yayi kwamishina a lokacin Mulkin Shekarau har guda biyu yayi Kwamishinan ruwa, sannan yayi na kananan hukumomi, a inda nan ma, aka yaba da irin rikon amanar sa, ta yadda Kananan Hukumomi suke karbar kasan su ba tare da fincen ko sisi ba.
Haka zalika babban abin da ya kara fito da shi kuma yake yawo a zukatan Kanawa shine Matatar ruwa da ya gina ta tamburawa wadda babu kamar ta a fadin yammacin Afirika, kuma sannan aka sami rarar kudi har Naira Miliyan dari biyar, amma ya mayar da su asusun gwamnati ba tare da ya zuba a aljihun shi ba.
A gefe guda wannan Dan takara sananne ne a jihar Kano, yayi takara har sau biyu, kuma sannan zai samu tausayin jama’ar kano saboda shine ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar PDP amma daga baya labari ya canja sakamakon waccen dama da aka bawa Kwankwaso.
Babban nakasun da wannan jam’iyyar za ta samu shine sabuwar jam’iyya ce, sai an tallata sosai kafin jama’a su san ta, sannan kuma jam’iyyar bata da wasu manya a cikin ta.
The post 2019 kujerar Gwamnan Kano allura ce a cikin ruwa – Adam Muhammad appeared first on Daily Nigerian Hausa.