2021: Najeriya Zata Samu Kanta Cikin Wadata – Satguru Maharaji
Najeriya za ta samu tarin wadata a bangarori da dama a shekarar 2021 da za a shiga.
Wannan shine wahayin da Satguru Maharaji na One Love Family ya saki.
Maharaji ya kuma yi hasashen ganin karshen matsalolin rashin tsaro da ya addabi Najeriya.
Satguru Maharaji Shugaban gidauniyar One Love Family ya saki wahayi mai dadin ji game da Najeriya, tattalin arzikinta da gwamnati gabannin shekarar 2021.
A cewar Maharaji, kasar za ta tsinci kanta a yanayin ci gaba da wadata ta kowani bangare na rayuwarta, musamman ta bangaren tattalin arziki, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Baya ga kaddamar da cewar kasar za ta daidaita ta fuskacin tattalin arziki a wannan shekarar, matsafin ya yi hasashen cewa lamarin rashin tsaro da kasar ke ciki a yanzu zai zama tarihi kwanan nan.
Sai dai kuma, don cimma haka, ya ba gwamnatin tarayya shawarar samar da tsarin kula da farashin abubuwa.
A bangaren siyasa, ya bayyana cewa a ci gaba da tsarin nan da baya rubuce a kundin tsarin mulki inda arewa ke mulkin shekaru takwas sannan ta mika wa kudu mulki.
Maharaji ya ce:
“Ba wai ina bayar da shawarar cewa dole ne sai wata kabila ta samar da Shugaban kasa a 2023 bane, amma na yarda cewa ya kamata mu sami shugaba da ke so da damuwa da al’umma.
“A ci gaba da yarjejeniyar da baya rubuce inda arewa ke mulki na shekaru takwas annan a mika mulki ga kudu.”