2021: Akwai Yiwuwar Za’ayi Karancin Abinci – Wani Malamin Jami’a

 

Shugaban Jami’ar Al-Hikmah ya ce akwai yiwuwar ayi karancin abinci.

Noah Yusuf ya ce kashe manoman da ake yi zai iya jawo wannan bala’i.

Yusuf ya bayyana ambaliyar ruwa da rigingimu a matsayin wasu dalilan Shugaban jami’ar Al-Hikmah, Ilorin, jihar Kwara, Farfesa Noah Yusuf, ya ce kisan da aka yi wa manoma, hadari ne ga samun isasshen kayan abinci.

Masanin ya ce bayan wannan kashe-kashe, za a ga tasirin ambaliyar ruwa da aka samu a wasu jihohi da kuma rikicin makiyaya da manoma da ake yi.

Farfesa Noah Yusuf yace wadannan abubuwa za suyi sanadiyyar jawo ci-baya ga nasarar da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu a harkar noma.

Tun ba yanzu ba kuma ana samun rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma, inda masu shuka ke zargin makiyaya da jawo masu asarar amfani.

Hakan na zuwa ne bayan an samu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe wasu manoma fiye da 40 a kauyen Zabarmari, karamar hukumar Jere, jihar Borno.

Yusuf ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida a garin Ilorin, jihar Kwara, wajen shirin bikin yaye wasu daliban da suka kammala karatu.

Shugaban jami’ar ta Al-Hikmah ya ce a shekarar nan za ayi bikin yaye dalibai ta kafar yanar gizo saboda annobar COVID-19 da ta takaita cakuduwar jama’a.

Farfesan ya koka game da halin da suke ciki, ya ce gwamnati ba ta ba makarantu masu zaman kansu gudumuwa ba duk da irin rawar da su ke taka wa.

A wannan shekara, Yusuf ya ce za su yaye dalibai 752, ciki akwai 18 da su ka samu matakin farko na Digiri. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here