2023: APC ta Kusa Bada Izinin Sayar da Fom Din Takara – Dr Salihu Lukman

A ranar Litinin, darekta janar na PGF, Dr Salihu Lukman, ya ce kwanan nan APC za ta fara sayar da fom din takara.

A cewarsa, ko shugaba Buhari bai da alhakin zabar dan takara, al’umma ne suke da wannan damar.

Ya ce, kowa zai iya siyan fom kuma ya fara kamfen don matsawar aka zabeshi, to shi za a tsayar.

A ranar Litinin, darekta janar na PGF, Dr. Salihu Lukman, yace fom din takarar jam’iyyar APC zai fita don duk masu neman wata kujera su nema, jaridar The Punch ta wallafa hakan.

Ya ce siyasa ta kunshi gasa ne, gasar da ake yi a siyasar da, yanzu ba a yinta. Ya sanar da manema labarai hakan a Abuja.

Lukman ya kula da yadda kungiyar ta dage wurin bunkasa. Ga dukkan alamu, PGF za ta tsayar da ‘yan takara nagari a matsayi daban-daban, a zaben 2023.

Ya ce ba jam’iyyar APC ko Shugaba Buhari ne zai bayar da umarnin inda za a bai wa damar tikitin ba.

Lukman ya ce, “Yanayin yadda APC take taka babbar rawa ya sanya kullum take samun karbuwa ta ko ina.

“Misali, kalli yadda hankalin kowa ya karkata a kan jam’iyyar, don a ga yadda za ta kaya a 2023 ko kuma wani zabe da zai zo.”

Yace idan a matsayinka na dan takara ba za ka iya dagewa wurin samun karbuwa a wurin mutane ba, to ya rage gareka.

“Abinda na ke so kowa ya sani shine, shugaba Buhari ba shi da alhakin zabar wani a jam’iyya, mutane ne keda wannan alhakin.

“Shiyasa mutane duk suna ta kiyasi, kowa da wanda yake zaton shi za a tsayar a zaben 2023, sai an tantance wanda zai tsaya takara a APC.

“Idan mutum dan siyasa ne, kawai ya fara kamfen, kowa zai iya samun nasara idan ya dage.” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here