2023: Cancanta ya Kamata Mubi a Zaben Shugaban Kasa – El- Rufai
Gwamna El-Rufai ya roki Najeriya da ta bar batun tsarin karba-karba wurin zaben Shugaban kasa.
Duk da dai A ranar Litinin, 23 na Nuwamba, Fashola ya bukaci a cigaba da yarjejeniyar karba-karba.
El-Rufai ya ce mulkin karba-karba ba zai gyara matsalolin da Najeriya take fuskanta ba.
Read Also:
Akasin kiran da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yayi na batun karba-karba tsakanin yankunan Najeriya wurin mulki, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce karba-karba ba zai taimaki Najeriya ba, ko kuma kawo karshen matsalolin da kasar nan take fuskanta ba.
Premium Times ta ruwaito yadda gwamnan yayi wannan jawabin a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, yayin da yake jawabi a kan yadda ‘yan Najeriya daga kowanne yanki suke kwadayin mulki, a taron NES.
El-Rufai ya ce batun karba-karba ba zai taimaki kasa ba.
Legit.ng ta tattara bayanai a kan yadda batun shugabanci karba-karba tsakanin arewa da
kudu ya zama al’ada tun da aka fara siyasa a 1999.
El-Rufai ya ce cancanta ya kamata a yi amfani dashi wurin zaben shugaban kasar Najeriya.