2023: Wata Kungiyoyi ta Nemi Wani Tsohon ‘Dan Majalisa da ya Nemi Kujerar Shugaban Kasa
Wasu su na burin ina ma Sanata Ken Nnamani ya karbi mulkin Najeriya.
Magoya bayan ‘Dan siyasar su na ganin shi ya fi cancanta ya gaji Buhari.
Nnamani, Tsohon ‘Dan Majalisa ne wanda yanzu ya na cikin manyan APC.
Kungiyoyin da ke goyon bayan Ken Nnamani a kasashen ketare, sun yi kira ga Sanata Ken Nnamani ya yi takarar kujerar shugaban kasa.
Wadannan magoya baya suna ganin cewa na-su ne ya fi dacewa ya nemi mulki daga kasar Ibo.
Jaridar Vanguard ta rahoto wadannan kungiyoyi suna cewa Ken Nnamani ya fi kowa dacewa da kujerar shugaban kasa saboda irin kwarewarsa.
Read Also:
Kungiyoyin sun kawo aikin da Nnamani ya yi a baya a majalisa, inda ya tsaya tsayin-daka wajen ganin an hana Olusegun Obasanjo sake zarcewa.
Shugaban wannan tafiya, Lawrence Odoemelam ya fitar da jawabi, ya na cewa Ibo su na burin ‘dan cikin su ya samu mulkin Najeriya a zaben 2023.
Mista Lawrence Odoemelam ya ce wanda ya dace da wannan kujera daga cikin Inyamurai shi ne Nnamani saboda wadannan dalilan da ya ambata.
Ya ce Nnamani ya taimaka wajen kafuwar mulkin farar hula, kuma ya nuna kwarewar shugabanci, sannan ya na cikin masu goyon-baya.
Odoemelam ya na ganin idan gwanin na su ya karbi shugabancin kasar nan a 2023, za a mulki ‘Yan Najeriya da bin dokar kasa, adalci, da gaskiya.
A 2003 ne Nnamani ya zama Sanata inda har ya yi nasarar zama shugaban majalisar dattawa tsakanin 2005 har zuwa karshen gwamnatinsu a 2007.