2023: Wasu Ministocin Buhari Suna Son Haye Kan Kujerarsa
Bayani da zafi ya nuna cewa wasu ministocin Buhari biyu suna zawarcin kujerarsa.
Kamar yadda aka gano, suna daga cikin wadanda suka assasa sauke Adam Oshiomhole.
An gane cewa basu son tsarin mulkin karba-karba na jam’iyyar APC yayi tasiri a 2023.
Duk da jan kunnen da aka yi na gujewa jan hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin mulkinsa, biyu daga cikin ministocinsa na zawarcin kujerarsa a shekarar 2023 mai zuwa.
Read Also:
Minsitocin da lamarin ya shafa su ake zargi da assasa tsige tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.
Hakazalika, a halin yanzu suna ta neman mafita domin samun cikar burinsu a karkashin jam,’iyyar APC din, jaridar The Nation ta wallafa.
Sun ja tunga sun tsaya tare da jan layi inda basu so a bada damar mulkin karba-karba na yanki da jam’iyyar APC ke so.
Tunda abin da a halin yanzu suka hararowa shine yadda za su haye kujerar mulkin kasar nan, sun nuna rashin amincewarsu na mulkin karba-karba.
Lokaci kadai ake jira inda ministocin biyu za su bayyana kansu.