Gwamnatin Najeriya ta Qaddamar da 3 ga Watan Mayu Matsayin Ranar Ma’aikata

 

Ma’aikatan Najeriya za su bi sahun sauran kasashen duniya don bikin ranar ma’aikata ta 2021.

Domin murnar ranar, gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin, 3 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga jama’a.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya taya ma’aikatan Najeriya murna tare da bukatan su da su kara jajircewa.

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 3 ga watan Mayu, 2021 a matsayin hutu domin bikin ranar ma’aikata ta duniya ta bana.

Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya yi sanarwar a madadin Gwamnatin Tarayya, ya taya ma’aikatan Najeriya murna saboda shaida bikin na bana, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya yaba musu kan haƙuri, fahimta da goyan baya da suke bayarwa wajen tafiyar da manufofi da shirye-shiryen mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na kai kasar zuwa ga mataki na gaba.

Aregbesola a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis daga Babban Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida, Shuaibu Belgore, ya yi kira ga ma’aikatan Najeriya da kungiyoyin kwadago da su kara himma da kishin kasa, yana mai cewa “matsalolin da ake ciki a yanzu zai wuce ba da dadewa ba saboda gwamnati ta himmatu wajen tsaron rayuka da dukiyoyin yan Najeriya duka.”

An yi wa sanarwar take da, ‘FG ta bayyana ranar Litinin, 3 ga watan Mayu, 2021 hutu don bikin ranar ma’aikata 2021. Ministan ya kara da cewa, “Gwamnati na sanya dukkan dabaru don dakile matsalolin rashin tsaro a kasar.

Don haka ina kira ga kungiyar kwadago da dukkan ‘yan kasa masu kishin kasa da su jajirce matuka a kokarin ganin bayan rashin tsaro.”

Aregbesola ya yiwa daukacin ma’aikatan Najeriya fatan yin bikin cikin zaman lafiya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here