Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya Amsa Gayyatar EFCC
Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Abdulaziz Yari ya shafe sa’o’i a babban ofishin EFCC a Garin Legas a jiya.
Ana zargin yunkurin fitar da kudi ya sa EFCC ta gayyaci Yari ya yi bayani.
Tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya dauki sa’o’i a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021, a hannun jami’an hukumar EFCC.
Jaridar Premium Times ta samu rahoto cewa an ga tsohon gwamnan a ofishin EFCC da ke titin Awolowo, Ikoyi, jihar Legas da kimanin karfe 11:00 na safe.
Read Also:
Alhaji Abdulaziz Yari ya hallara ofishin EFCC ne domin amsa goron gayyatar da aka aika masa. Majiyar jaridar ta bayyana cewa Abdulaziz Yari ya fada hannun EFCC ne bayan ya yi yunkurin karkatar da Naira biliyan 300 daga asusun wani kamfani.
Kawo yanzu jaridar ba ta samu cikakken labarin abin da ya wakana ba, amma kokarin ‘dan siyasar na zarar wannan kudi ta wani banki bai iya yiwuwa ba.
Da ya shiga hannun EFCC, tsohon shugaban gwamnonin na Najeriya ya ba hukumar EFCC dogon jawabi, daga baya aka sallame shi da maraicen ranar Talatar.
Ta tabbata cewa Abdulaziz Yari ya bar ofishin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa a jiya, har ya yi waya da mutane.
Amma alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a sake kiran tsohon gwamnan, kuma daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC domin ya amsa wasu tambayoyin.
Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa Yari ya ziyarci ofishinsu, amma bai yi karin bayani kan lamarin ba.