Fitaccen Mawaki,Eedris Abdulkarim ya Mika Godiya ga Matarsa Kan Bashi Kyautar Kodarta
Sanannen mawakin gambara, Eedris Abdulkarim, ya mika godiyarsa ga Ubangiji kan nasarar da aka samu wurin aikin dashen kodar da aka yi masa.
Bai tsaya a nan ba, ya kwararo kalaman soyayya da bayyana tsabar kaunar da yake wa matarsa kan sadaukarwar da tayi masa ta hanyar bashi kodarta.
Ya mika godiya ga ‘yan uwa, abokai, masoya da duk masu masa fatan alheri inda yace nan babu jimawa zasu dawo gida garas.
Fitaccen mawakin gambara, Eedriss Abdulkareem, ya mika godiyarsa ga matarsa Yetunde kan bashi kyautar kodarta da tayi kuma aka samu nasarar yi masa dashe.
Mawakin ya bayyana godiyarsa ne a wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram a ranar Laraba inda ya kara da cewa zai kaunace tare da sonta a koda yaushe.
Idan za tuna, kamfaninsa na nishadantarwa ya bada bayani kan lafiyar mawakin a ranar Litinin.
Read Also:
A wata takarda da Honarabul Myke Pam ya fitar, yace an samu nasarar yi wa mawakin dashen kodar.
A yayin jawabi da kansa, Abdulkareem ya mika godiyarsa ga Ubangiji da kuma dukkan mutanen da suka taimaka aka samu nasarar aikin.
Mawakin gambaran ya rubuta:
“Nagode Ubangiji. Ina mika godiya ga Ubangiji madaukaki da aka samu nasarar aikin dashen kodata a cikin ranakun karshen mako. Sunanshi zai cigaba da daukaka har abada.
“Kalamai ba zasu iya bayyana irin kaunata da sadaukarwata ga matata Yetunde, wacce Ubangiji ya cikasa rayuwata da ita, nake mata ba. Masoyiya, zan cigaba da kaunar ki har abada.
“’Ya’yana, Ubangiji ya karba addu’o’inku. Mama da Baba zasu dawo gida cikin koshin lafiya nan babu dadewa.
“Ga ‘yan uwana, kamfanin nishadantarwa Lakreem, abokai, masoya da masu min fatan alheri, ina cewa Allah ya duba mana, zan kuma sake ganinku nan babu dadewa.
“Na mika wannan sakon godiyan nen na farko domin godewa Ubangiji kan ni’imar da yayi mana.”