Sanata Abdullahi Adamu ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC
Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam’iyyar bayan duka waɗanda suke takarar sun janye wa Abdullahi Adamu.
Read Also:
Kafin sanar da shi a matsayin sabon shugaban, sai da Gwamna Badaru ya tambayi wakilan zaɓe ko kuma deliget kan cewa sun amince da Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban APC, sai suka ce sun amince.
Tun kafin a soma taron dama ana ta raɗe-raɗin cewa za a samu maslaha a ba Abdullahi Adamu shugabancin, inda a yayin taron ne masu takarar suka sanar da cewa duk sun janye.