ALLAH ya yi wa Tsohon Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Maikano Rabiu Rasuwa

 

Allah ya yi wa Alhaji Abdullahi Maikano Rabiu rasuwa.

Tsohon dan majalisar ya rasu a ranar Alhamis yana da shekaru 72 a jahar Kano.

Rabiu, wanda za a binne daidai da koyarwar addinin Islama, ya rasu ya bar yan uwa, yara da mata Mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jahar Kano sun shiga halin juyayi sakamakon mutuwar tsohon dan majalisa, Dr Abdullahi Maikano Rabiu.

A cewar jaridar The Punch, tsohon dan majalisan wakilan ya rasu sakamakon cutar COVID-19 a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu.

Rabiu ya rasu a cibiyar killace masu cutar da ke Kwanar Dawakin Tofa, a Kano, inda yan uwansa suka tabbatar da mutuwarsa ga manema labarai a ranar Alhamis.

“Tare da nauyin zuciya da tawakkali ga Allah madaukakin sarki muna bakin cikin sanar da mutuwar shugaba kuma ma’assashin wannan gidauniya. Muna addu’a kan Allah ya yafe masa zububansa da kuma bashi babban wuri a Al-jannah madaukakiya.

Allah ya sa ka huta Dallatu.” Rabiu wanda ya kasance tsohon mai ba tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau shawara kan harkokin tattalin arziki ya riki mukaman siyasa da dama a rayuwarsa.

Ya mutu yana da shekaru 72 a duniya kuma za a binne shi daidai da koyarwar addinin Musulunci a garinsa na Dawakin Tofa.

Tsohon dan majalisar ya mutu ya bar matar aure daya, yara da yan uwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here