Jami’ar Jahar Abia ta Rasa Malamanta 3 Lokaci Guda

 

An shiga yanayin ruɗani da jimami a jami’ar jahar Abia yayin da malaman makarantar uku suka kwanta dama a rana ɗaya.

Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba’a gano musabbabin mutuwar malaman uku ba, cikinsu harda Farfesa.

Sai dai wani da ya nemi a sakaya sunasa yace malaman jami’ar na cikin wani hali, domin rabon su da albashi tun watan Janairu.

Abia – Jami’ar jahar Abia dake Uturu, ta shiga yanayin tashin hankali da jimami biyo bayan mutuwar lakcarori uku cikin awanni 24, kamar yadda punch ta rawaito.

Wata majiya daga jami’ar ya bayyana cewa lakcarorin sune, Farfesa A. I. Nwabughuogu na tsangayar tarihi, dakta D. S. Okoroigwe da kuma Dakta Osince Okike na sashin koyar da ilimin siyasa a kimiyyance.

Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba’a gano musabbabin mutuwar malaman jami’ar ba.

Wane hali malaman jami’an suke ciki?

Hakanan kuma majiyar ya ƙara da cewa malaman jami’ar sun shiga wani matsanancin hali na rashin kuɗaɗen shiga domin an jima ba’a biyasu albashi ba.

Yace:

“Muna bin bashin albashi na sama da watanni bakwai, karo na karshe da aka bamu haƙƙin mu shine a watan Janairu, 2021.”

ASUU Ta tabbatar da mutuwar malaman

Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU reshen jami’ar jahar Abia, Dakta Victor Nkemdirim, ya tabbatar da mutuwar malaman guda uku.

Shugaban na ASUU ya bayyyana lamarin mutuwar malaman cikin awanni 24 da mara daɗin ji da kuma rashin sa’a.

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Abia, Chijioke Nwogu, game da lamarin ya ci tura domin wayarsa ta ƙi shiga.

Bugu da ƙari har zuwa yanzun da aka rubuta wannan rahoton kakakin yan sandan bai maido da amsar sakonnin karta kwana da aka tura masa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here