Hana Cajin Waya: Gwamnati Katsina Zata Datse Hanyoyin Sadarwa a Kananan Hukumomi 3 Dake Jahar

 

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shirin gwamnatinsa na datse hanyoyin sadarwa a wasu kananan hukumomi.

Masari yace waɗannan matakai da ake ɗauka zasu shafi mutane a hanyar cin abincinsu amma ya zama wajibi.

Gwamnan ya kuma sanar da hana cajin waya a faɗin kananan hukumomi 19 daga cikin 34 dake Katsina.

Katsina – Gwamna Aminu Bello Masari na jahar Katsina, yace gwamnatinsa na duba bukatar datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomin Funtua, Bakori da Malumfashi, kamar yadda This Day ta rawaito.

Gwamnan yace zai ɗauki wannan matakin ne a wani ɓangare na kokarin dakile ayyukan yan bindiga a jahar.

Masari ya bayyana haka ne ranar Litinin, yayin ƙaddamar da kwamitin da zai saka ido kan sabuwar dokar tsaro da gwamnan ya sawa hannu a gidan gwamnati.

Shin dagaske Gwamnatin Katsina ta hana cajin waya?

A wani cigaban kuma, gwamna Masari ya sanar da hana yan kasuwa masu cajin waya a ƙananan hukumomi 19 cikin 34 dake faɗin jahar.

Channels TV ta rawaito Masari na cewa:

“Muna da yakinin cewa wannan wani ɓangare ne da ke taimakawa yan bindiga wajen samun isasshen sadarwa.”

An hana siyar da man fetur a wasu yankuna

Gwamnan yace matakan da gwamnati ke ɗauka ko shakka babu zai shafi kuɗin shigar al’umma amma ya zama wajibi ne a halin yanzu.

Bugu da kari Masari yace waɗannan matakan zasu taimaka wajen hana yan fashi amfani da sabis na sadarwa da wasu abubuwan more rayuwa.

A jawabinsa yace:

“Muna da yakinin cewa da wannan matakin da kuma wanda muke shirin ɗauka tare da ma’aikatar sadarwa zasu taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin mu.”

“Mun dakatar da siyar da man fetur a Funtua, Bakori da Malumfashi, kuma muna duba yuwuwar datse sauran hanyoyin sadarwa a waɗannan ƙananan hukumomin.”

A cewar gwamna Masari, ya kamata mutane su gane cewa babban abokan gaba sune masu baiwa yan ta’addan bayanai saboda haka ya zama wajibi a magance su a sahun farko.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here