Abin Fashewa da Boko Haram ta Dasa ya yi Sanadiyyar Mutuwar Wasu Sojoji

 

An rahoto cewa mayakan Boko Haram sun kashe sojoji uku a jihar Borno.

Jami’an tsaron na Najeriya sun mutu ne bayan sun shiga abubuwan fashewa da yan ta’addan suka binne a karkashin kasa.

An tattaro cewa sojoi da dama sun ji munanan raunuka a lamarin da ya lalata motocin sojin gaba daya.

Akalla jami’an rundunar sojin Najeriya uku ne suka mutu sakamakon tashin abubuwan fashewa da yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka dasa a karkashin kasa.

A bisa ga rahoton kafar labarai abun dogaro, an kashe sojojin ne a hanyar Maiduguri/Gomboru a ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, lokacin da ayarin motocin rundunar bataliya ta uku suka yi tawo mu gama da abubuwan fashewar.

An tattaro cewa sojojin na raka matafiya tsakanin Gomboru Ngala da Dikwa lokacin da suka yi tawo mugama da abubuwan fashewar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum uku da jikkata wasu da dama.

Wani soja da abun ya faru a idonsa ya ce motocin, wanda ke dauke da sojoji, ya lalace ta yadda ba za a iya gyarawa ba.

“Motarsu na yaki ya lalace fiye da tsammani sannan mun rasa wasu sojoji sakamakon tashin abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa a hanyar Dikwa/Gomboru da Ngala.

“Addu’anmu da tunaninmu na tare da iyalansu. Abun bakin ciki ne, mun rasa sojoji uku saboda abun fashewa.”

Rundunar sojin Najeriya bata fitar da kowani sanarwa kan mutuwar sojojin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here