Abinda ke Damun El-Rufa’i – APC

 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce ɗimuwar rashin samun kujerar minista ce har yanzu ke damun tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jam’iyyar ta fitar a matsayin martani ga kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce jam’iyyar ta bar muradun da aka kafa ta akai wanda ya sa shi ficewa daga cikinta zuwa jam’iyyar SDP.

“El Rufa’i ya faɗi ainihin dalilinsa na nuna damuwa, inda a cewarsu saboda bai ji daɗin yadda shugaba Tinubu da gwamnatinsa suka yi mishi ba kan batun rasa kujerar zama minista, kuma domin ya kare mutuncinsa, shi ne yake sukar jam’iyyar da ta kai shi ga nasara a siyasa.” In ji sanarwar.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa ƴan Najeriya na da tunani fiye da yadda El Rufa’i ke musu kallo, kuma sun san cewa son kanshi kawai yake yi ba wai tsantsar damuwa kan ƙasar ba ne.

Sanarwar ta kuma jam’iyyar APC ba ta damu da mataki ko kalaman El Rufa’i ba, kuma suna ci gaba da tarbar sabbin miliyoyin mutane masu shiga jam’iyyar a fadin ƙasar waɗanda ke shiga saboda muradun jam’iyyar masu kyau da kuma goya wa shugaba Tinubu baya kan tsare-tsarensa da ke kawowa ƙasar cigaba.

APC ta kuma ce kiran da ya yi wa sauran ƴan adawa su shiga jam’iyyar SDP, ba komai ba ne illa tsantsar yaudara da ƙeta da kuma ƙoƙarin biyan buƙatun kai.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here