Olusegun Obasanjo ya Bayyana Abinda Yake Haddasa Fitina a Najeriya
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce yawan mutanen Najeriya ne kan gaba wajen haddasa fitina a kasar.
A cewarsa, wannan yana taimakawa wajen daukar matasa marasa aikin yi domin aikata laifuka.
A sakamakon haka, Obasanjo ya ce Najeriya na cikin babbar matsala idan ba za ta iya samar wa matasa aikin yi ba.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan aikata laifuka a Najeriya.
A cewarsa, ta’addanci, fashi da makami na karuwa a Najeriya sakamakon karuwar yawan mutanen kasar. A zahirin gaskiya, tsohon shugaban kasar ya ce wannan yana hana shi barci cikin dare.
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoton kungiyar cigaban Afirka ta 2020 (APG) a Legas mai taken: ” Making Africa’s Population an Asset”, jaridar Guardian ta ruwaito.
Read Also:
Obasanjo ya dage cewa dalilin tayar da kayar baya da ta’addanci a kasar bai yi nisa da kasancewar akwai tarin matasa marasa aikin yi da ake daukar su cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da kungiyoyin masu aikata laifuka.
Ya ce:
“An ce Mohammed Yusuf wanda ya fara Boko Haram mutum ne mai nagarta da sanin yakamata tare da dimbin matasa marasa aikin yi da ke jira domin su saurare shi. Na ji akwai lokacin da ya kira mabiyansa ya ce wa daya, ‘ka je jami’a, shekaru nawa yanzu da ka kammala?’ Ya ce shekara uku kuma me kake yi yanzu? Ya ce, ‘babu aiki.’ Sannan ya amsa, ‘ka ga rashin amfanin ilimin jami’ar ka.”
“Ta haka ne kalmar Boko Haram ta bullo. Ta hanyar mabiyansa ba su da ayyukan yi, ya ce ‘kun ga rashin amfanin ilimin ku na boko.’ Idan ba za mu iya samar da ayyukan yi ga yawan mutanen mu ba, da gaske muna cikin matsala. Babu bukatar wani ya gaya mana wani abu.”