Hukumar ‘Yan Sandan Jahar Zamfara Sun Ceto Mutane 12 Daga Hannun ‘Yan Bindiga

 

‘Yan sanda sun samu nasarar kwato mutum 12 hannun ‘yan bindiga.

Wannan ya biyo bayan bidiyon daliban da aka sace a kwalejin noma.

Gwamnatin Zamfara ta lashi takobin ceto wadanda aka sace.

Zamfara – Hukumar ‘yan sandan jahar Zamfara ta samu nasarar ceto mutum 12 da yan bindiga suka sace a jahar Zamfara, kakakin hukumar Mohammed Shehu ya bayyana.

A jawabin da Shehu ya saki ranar Laraba, ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka ceto akwai shugaban masu gadin kwalejin ilmin kiwon lafiya dake Tsafe, jahar Zamfara.

Rahoto TheCable ya nuna cewa an yi awon gaba da shi ne da safiyar Laraba. Shehu ya kara da cewa a harin ceto da suka kai, jami’an yan sanda sun samu nasarar ceto wasu mutum 11 da aka sace ranar 12 ga Agusta, 2021.

Yace:

“Mun samu labarin cewa asu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 11 a kauyen Yarkofoji, dake karamar hukumar Bakura ranar 12 ga Agusta, 2021.”

“Bayan haka, hukumar ta samu nasarar ceto shugaban masu tsaron kwalejin fasahar kiwon lafiya dake Tsafe.”

Kakakin yan sandan ya kara da cewa an garzaya da wadanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu kafin mayar da su wajen iyalansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here