Satar Amsa a Jarabawa: Nasarawa Poly ta Sallami Dalibai 51

 

An sallami akalla dalibai 51 daga makaranta kan laifin sata a jarabawa.

Shugaban makarantar ya yi kira ga dalibai su yi watsi da satar amsa a jarabawa.

Wannan ya biyo bayan sallamar dalibai biyu da aka kan shiga kungiyar yan daba.

Nasarawa – Hukumar makarantar fasaha ta jahar Nasarawa watau Naspoly ta fittitiki dalibar 51 kan laifin satar amsa a jarabawar da aka gudanar a kakar karatun 2019/2020.

Mai magana da yawun makarantar, Uba Maina, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, rahoton NAN.

Mana yace kwamitin ingancin ilimi na makarantar ta amince da a sallami daliban.

Ya lissafa daliban tsangaya-tsangaya da aka sallamar, daga cikinsu har da dalibai aikin jarida.

Yace:

“An sallami daliban ne kan laifuka daban-daban da ya shafi jarabawa. Cikinsu akwai masu zaune a makaranta kuma akwai yan jeka-ka dawo.”

“Daliban da aka sallama na karatun karamin Difloma ne ND da babban Difloma HND a tsangayar Injiniyanci, Akawun, aikin jarida, dss.”

Mana ya kara da cewa shugaban makarantar, Abdullahi Ahmed, ya umurci daliban da aka kora sun mika dukkan dukiyar makaranta dake hannunsu wa shugabannin tsangayarsu.

Ya yi kira ga dalibai su yi watsi da satar amsa a jarabawa kuma su daina bin abokan banza don cigaban makarantar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here