Abu 4 da Majalisar Wakilai a Najeriya ta Sasanta Tsakanin ASUU da Gwamnati a 2021
A watan Nuwamban 2021 Majalisar Wakilai ta Najeriya ta shiga tsakanin ƙungiyar ASUU ta malaman jami’a da kuma gwamnatin tarayya, inda suka cimma matsaya kan abu huɗu na buƙatun ƙungiyar.
Read Also:
Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci zaman kuma ministocin kudi da na ilimi ne suka wakilci ɓangaren gwamnati a tattaunawar.
Abubuwan da suka cimma su ne:
Farfado da jami’o’i
Biyan kudin alawus
Tsarin biyan albashi na IPPS
Sauran ƙorafe-ƙorafe
A lokacin, Shugaban Kwamitin Majalisa kan Manyan Makarantu Aminu Sulaiman Goro ya faɗa wa BBC Hausa cewa an samu fahimtar juna a tsakanin duka ɓangarorin, kuma an daidaita da malaman jami`ar ta yadda ba sauran fargaba game da barazanar yajin aikin da ƙungiyar ke yi.