Abubuwa 6 Game da Harin NDA

 

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai mumunan hari makarantar horar da Sojin Najeriya NDA dake jahar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa ‘yan bindigan sun hallaka mutum biyu yayinda suka yi awon gaba da jami’in Soja guda daya.

An tattaro cewa ‘yan bindigan sun kai farmakin ne misalin karfe 1 na dare.

Ga abubuwa 6 da ya kamata ku sani:

1. Yan bindigan sun samu shiga makarantar ne ta katanga kuma suka tafi rukunin gidaje kai tsaye suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

2. Sun yi awon gaba da Soja mai suna Manjo Datong.

3. Sun kashe Hafsoshi biyu; Laftanal Cadre Wulah da Flt Lt CM Okoronwo.

4. Wani Soja mai suna Lt Onah ya jikkata kuma yana jinya a asibiti.

5. ‘Yan bindigan sun kira, sunce suna bukatar N200m kudin fansa.

6. Sojojin Najeriya sun lashi takobin nemo wadannan yan bindiga tare da ceto Sojan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here